Gwamnati za ta kidaya masu bukata ta musamman

Yau Talata 3 ga watan Disamba ake bikin ranar masu bukata ta musamman

Majalisar dinkin duniya ce ta ware ranar domin tunatar da gwamnatoci da sauran al’umma kan hakkin da ke kansu na kulawa da masu bukata ta musamman.

Wani binciken hukumar lafiya ta duniya yace zuwa 2020 akwai masu bukata ta musamman kusan miliyan 27 a Najeriya, 15% kenan na yawan al’ummar kasar, ko kuma a duk mutum bakwai guda mai bukata ta musamman ne.

Taken bikin na bana shine daga likkafar shugabannin kungiyoyin masu bukata ta musamman domin damawa dasu a fannin cigaban kasa

Shugaban cibiyar kula da masu bukata ta musamman Ayuba Gufwan a ranar litinin yace gwamnati zata gabatar da shirin kidayar masu bukata ta musamman ta hanyar amfani da yanar gizo.

Yace cibiyar zata hada hannu da hukumar kidayar jama’a ta kasa wajen wannan aiki, wanda za a yi shi a duk fadin kasa.
Gufwa yae hakan zai aiwa gwamnati damar sanin hakikanin yawan masu bukatata musaman a kasar nan da kuma yadda za a taimaka musu.

Masu bukata ta musamman a Kano dai na kokawa kan yadda suka ce gwamanti Abba Kabir Yusif bata damawa dasu, la’akari da ba wani mukami da suka rabauta dashi a gwamnatance.

Gwamnati za ta kidaya masu bukata ta musamman

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *